An girke jiragen da za su yaki ’yan bindiga a Sokoto

An girke jiragen da za su yaki ’yan bindiga a Sokoto

Jiragen yakin sojin saman Najeriya sun isa jihar Sakkwato domin yakar ’yan bindigar da ke addabar jihar a baya-bayan nan.
Kakakin rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola ya ce tuni babban Hafsan rundunar, Air Marshall Sadique Abubakar ya ziyarci jihar domin lura da yadda za a yaki maharan.

Air Marshall Sadique ya kuma tattauna da manyan kwamandojin rundunar da za su jagoranci yakin murkushe ‘yan bindigar.

Shugaba Buhari ya umarci sojoji da su gaggauta magance ta’addancin ’yan bindiga masu addabar jihar Sokoto.
Domin Samun zafafan labaran da muke sakawa a TWITTER taba Nan
Umurnin na zuwa ne bayan Gwamnan Jihar, Aminu Tambuwal ya nemi daukin Gwamantin Tarayya wurin kawo karshen kan aika-aikan maharan.

Gwamnan ya nemi daukin ne bayan harin ’yan bindiga da ya yi ajalin akalla mutum 74 a Karaman Hukumar Sabon Birni a makon jiya. 


Domin Samun zafafan labaran da muke sakawa a FACEBOOK taba Na

Leave a Reply

Your email address will not be published.