Majalisa ta ki yarda da hukuncin danda’ke masu fyade Amma ta nemi a yanke musu daurin Rai da rai

Majalisa ta ki yarda da hukuncin danda’ke masu fyade, Amma ta nemi a yanke musu daurin Rai da Rai

Majalisar wakilan Najeriya ta ki amincewa da dokar neman zartar da hukuncin danda’ke wadanda aka samu da laifin aikata fyade.
Mambobin majalisar sun nuna rashin amincewarsu da dokar yayin tattauna yawaitar aikata fyade ga mata a zaman majalisar na yau Alhamis.
Mista James Faleke, mamba a majalisar wakilai daga jihar Legas, ya nemi majalisar ta amince da hukuncin danda’ke duk wanda aka samu da laifin aikata fyade.
Tun kafin ya tambayi ra’ayin sauran mambobin majalisar, Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai, ya tambayi Faleke cewa; “me zai faru ga babbar macen da tayi wa karamin yaro fyade?”
Tambayar ta Gbajabiamila ta haifar da barkewar surutu a zauren majalisar.
Bayan ya tambayi ra’ayin ‘yan majalisar a kan dokar, sai sukayi ihun basu amince da ita ba.
Duk da haka, majalisar ta saka dokar ta baci a kan yawaitar aikata fyade ga ‘ya’ya mata tare da neman zartar da hukuncin daurin rai da rai ga ma su aikata laifin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.