Majalisa ta nemi a karo Dakarun sojoji 100, 000 a Najeriya

Majalisa ta nemi a karo Dakarun sojoji 100, 000 a Najeriya

 
Majalisar wakilan tarayyar Najeriya ta yi kira ga jami’an tsaron Najeriya su kara daukar sojoji 100, 000 domin a rufe gibin da ake dashi na rashin isassun dakaru wajen yaki da ta’addanci.
‘Yan majalisar wakilan kasar Nan sun yi kira da cewa a kara yawan sojoji a Najeriya. 
Majalisar ta ce wannan zai taimaka wajen samun nasara a yakin da ake yi da tsageru da ‘yan ta’adda.
Bayan haka majalisar ta nemi sojojin kasa su dawo da jami’an da sukayi ritaya, a ajiye su idan bukata ta tashi. 
Wannan ya na cikin sashe na 25 a kashi na 7 na dokokin gidan soja.
‘Yan majalisar sun bada sharadin cewa ka da sojojin da za a maido aiki su zarce shekaru 50, sannan kuma su zama cikin koshin lafiya da karfin jiki ta yadda za su iya yin amfani a yaki.
Wannan kira ya zo ne daga bakin kwamitin majalisar wakilai a kan harkar sojojin kasa bayan kwamitin ya yi bincike game da harin da Boko Haram takai kwanaki a garin Auno.
Shugaban wannan kwamiti dake kula da sojojin kasa, Honarabul Abdulrazak Namdaz ne ya gabatar da rahoton binciken kwamitin a zauren majalisa a zaman farko na makon nan.
Da yake magana game da mummunan harin da aka kai a Auno, Abdulrazak Namdaz ya ce jami’an tsaro basu bada isasshen kariya ga matafiyan da suka fada hannun ‘yan ta’ddan ba.
Namdaz yake cewa an samu matsala ne: “Saboda sojojin kasa ba su da isassun dakarun da za su rike wuta na tsawon lokaci bayan sun lallasa ‘yan Boko Haram a wasu kauyuka.”
“Wannan ya sa ake tarwatsa rundunar sojin domin a kafa tawaga mai karfi. Idan har aka dauki sojoji rututu aiki, babu bukatar a rika kafa wata tawaga ta musamman” inji Namdaz.

Leave a Reply

Your email address will not be published.