Majalisar wakilai ta yi wa shugabannin tsaro kiran gaggawa

Majalisar wakilai ta yi wa shugabannin tsaro kiran gaggawa

Majalisar wakilai ta yanke hukuncin yi wa shugabannin tsaro kiran gaggawa sakamakon hauhawar rashin tsaro a kasar na.
Shugabannin tsaron sun hada da: Mai bada shawara ga shugaban kasa a kan tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno, shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Gabriel Olonisakin.
Sauran sune sifeta janar din ‘yan sanda, Mohammed Adamu da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya, Yusuf Bichi.
An yi kiran gaggawar ne bayan bukatar da Sada Soli ya mika gaban majalisar na yin hakan sakamakon hauhawar al’amuran ‘yan bindiga a yankin arewa ta tsakiya da arewa maso gabas.

Leave a Reply

Your email address will not be published.