Gobara ta tashi a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja

Gobara ta tashi a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja

Gobara ta tashi a Fadar Shugaban Najeriya ta Aso Rock da ke Aduja.
Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kasa kan yada labarai Garba Shehu shine ya tabbatar da hakan.
Gobarar ta tashi ne a cocin fadar gwamnati sakamakon tartsatsi da kayan wutar lantarki suka yi.
“Amma daga baya kuma jami’an kwana-kwana sun kashe wutar,” inji shi.
Garba Shehu ya kuma tabbatar da cewa ba a sami wata asara me yawa ba sakamakon gobarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.