Kotun Koli ta tabbatar da tube Aminu Babba Dan-Agundi daga matsayin hakimin Gabasawa sarkin Dawaki Mai tuta

Kotun Koli ta tabbatar da tube Aminu Babba Dan-Agundi daga matsayin hakimin Gabasawa sarkin Dawaki Mai tura

Kotun kolin Najeriya ta jaddada tube rawanin tsohon Sarkin Dawaki Mai tuta kuma hakimin Gabasawa, Alhaji Aminu Babba Danagundi.
Marigayi tsohon sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ne ya tube rawanin hakimin Gabasawa kuma Sarkin Dawaki Mai tuta a shekarar 2003.
Da take karanta hukuncin, Mai Shari’a Mary Odili ta ce an yanke wannan hukuncin ne bisa la’akari da kudurin da alkalai biyar na kotun suka hadu a kai.
Hukuncin na zuwa ne shekaru shida bayan rasuwar Alhaji Ado Bayero.
A shekarar 2003 ne marigayin ya tube wa Aminu Babba Dan-Agundi rawaninsa bisa zargin rashin da’a da shugaban lamarin siyasa.
An zarge shi da rashin biyayya ne dai bayan da marigayin ya gayyace shi fada, amma bai je ba.
Za a fara bi gida-gida domin gwajin cutar Korona a kano
Bayan tube shi ne ya kai karar Sarkin da Masarautar Kano wata babbar kotu, inda Alkali Sadi Mato ya yanke hukuncin a dawo da shi, a kuma biya shi dukkan hakkokinsa.
Bayan tube shi ne ya kai karar Sarkin da Masarautar Kano wata babbar kotu, inda Alkali Sadi Mato ya yanke hukuncin a dawo dashi, a kuma biya shi dukkan hakkokinsa.
Daga nan ne Masarautar ta Kano ta daukaka kara, itama kotun daukaka karar ta tabbatar da hukuncin babbar kotun na a dawo dashi.
A karshe Masarautar Kano ta garzaya kotun koli, wadda ta tabbatar da matakin da marigayi Sarkin Kano Alh Ado Bayero ya dauka na korar Aminu Babba Dan-Agundi daga mukamin hakimin Gabasawa, Sarkin Dawaki Mai tuta.
Majalisar dattawa zata binkici Naira triliyan daya da Bilyan Dari takwas da Najeriya ta bayar domin Samar da wutar lantarki
Marigayi Alhaji Ado Bayero ya nada Alhaji Aminu Babba Danagundi a matsayin Sarkin Dawaki Maituta kuma hakimin Gabasawa a shekarar 1999.
Danagundi ya kwashe shekara 13 a kan karagar mulkin kafin al’amari tsakaninsa da marigayin sarki ya rincabe har ya tube masa rawani.
An maye gurbinsa da Sarkin Dawaki Maituta na yanzu, Alhaji Bello Tuta.
Majalisar wakilai ta nemi a Kara daukar sojoji dubu Dari a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published.