Majalisar dattawa za ta binkici Naira triliyan daya da Bilyan Dari takwas da FG ta bayar domin samar da wutar lantarki

Majalisar dattawa za ta binkici Naira triliyan daya da Bilyan Dari takwas da FG ta bayar domin samar da wutar lantarki

Majalisar dattawan Najeriya za ta binkici kudaden da gwamnatin tarayyar ba bawa bangarorin Samar da wutar lantarki Wadanda tun farko an siyar dasu ga Yan kasuwa, Wanda kudaden sunkai Naira triliyan daya da Bilyan Dari takwas (1,800,000,000,000 ) tsakanin shekarar 2013 zuwa yanzu.

A cewar rahotan Kwamitin Majalisar na kula da harkokin samar da wutar lantarki, zai gudanar da Zama na musammam, na kwanaki uku domin gano yadda aka sarrafa kudaden.
Domin Samun zafafan labaran da muke sakawa a TWITTER taba Nan
A shekarar 2013 ne gwamnatin ta fara Sanya kudaden a bangaren wutar lantarki, wanda Majalisar tace zuwa yanzu ya kai Naira triliyan daya da Bilyan Dari takwas (1,800,000,000,000 ) 
Da yake zantawa da manema labarai shugaban Kwamitin kula da Samar da wutar lantarki na Majalisar dattawa sanata gebriiel susuwam, ya ce ba Wai za suyi bincike bane, don yin bita da kuli ga wani, Sai Dan Ganin an sarrafa kudaden ta hanyar da yakamata.
Domin Samun zafafan labaran da muke sakawa a FACEBOOK taba Na
A cewar sanata Gebriiel susuwam, anrika sakin kudaden kashi-kashi ne, inda a kasan farko, gwamnati ta bada Naira Bilyan Dari bakwai 
( 700,000,000,000 ) inda daga bisa ni, aka Kara Naira Bilyan Dari shida 
( 600,000,000,000 )
Sannan Kuma Gwamnati ta bada Naira Bilyan Dari uku da tamanin
 ( 380,000,000,000 ) kafin daga bisani asake Basu Naira Bilyan Dari biyu da goma Sha uku ( 213,000,000,000 )
Ya ce Minister kudi Zainab Ahmad da takwaranta na lantarki da sauran hukumomin gwamnati masu Alaka da lantarki suna daga cikin wadanda zasu kawo cikakkun bayanai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.