Za a fara bin gida-gida don yin gwajin cutar Korona a kano.

Za a fara bin gida-gida don yin gwajin cutar Korona a kano

Gwamnatin jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya ta ce za ta fara bi gida-gida domin yi wa al’ummar jihar gwajin cutar korona.
Gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne, ya bayyana Hakan a ranar Alhamis a yayin wata ganawa da manema labarai don bayar da bayanai a kan halin da ake ciki a yaki da cutar Coronavirus a jahar.
Ganduje ya ce duk da matakan da gwamnatin  jahar ke dauka kan dakile yaduwar cutar korona, yin gwajin don gano masu dauke da cutar zai taimaka wajen samun nasarar kawo karshen cutar a kan lokaci.
Gwamnan ya ce, kasancewar akwai kananan hukumomi uku da suka fi yawan masu cutar a jihar, shi ya sa aka dauki wannan mataki na bin gida-gida don gwaji, musamman a kananan hukumomin da abin yafi kamari.
Ganduje ya ce kananan hukumomin su ne Nasarawa da Tarauni da kuma Municipal.
Ganduje ya Kara da cewa tun da farko an fada mana cewa, wannan ciwo  ba’asan lokacin da zai tafi ba, saboda Haka Dole ne mu koyi yadda Zamu zauna da wannan ciwo, ba tare da ya ka mamu ba.
Yace mun riga munga hanyoyin uku, dake Hana wannan ciwo yaduwa, Wanda muka dauke su, su ne turba domin bi a Koda da  yaushe, domin gujewa wannan ciwo.
Domin Samun zafafan labaran da muke sakawa a TWITTER taba Nan
A na sa bangaren Shugaban kwararrun Likitoci na Kwamitin Kar ta kwana, Mai ya ki da cutar Korona na jiha, Dakta Tijjani Husaini, ya ce masu dauke da wannan cuta, sun fito daga kana nan hukumomi 30 daga cikin kana nan hukumomi 44 da ake dasu a Jihar kano.
Ya ce Kashi casa’in 90% na Masu dauke da cutar sun fito daga  kana nan hukumomi Tara,  takwas daga  cikin kana nan hukumomin kwaryar birnin Kano da kawaye, wanda ya hada da Tarauni, Nasarawa, Gwale, Dala, Kumbotso, Kano Municipal da Kuma yankin karamar hukumar Karaye.
Ya Kara cewa Mazabar gyadi-gyadi ta Arewa itace tafi ko’ina yawan Wadanda suka kamu da wannan cuta a Tarauni.
Domin Samun zafafan labaran da muke sakawa a shafimmu na FACEBOOK taba Na
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya shaida wa BBC cewa adadin mutanen dake kai kansu asibiti domin a gwada su a Kano ya yi kasa shi ya sa gwamnati taga ya dace a fara wannan gwaji ta hanyar bin gida-gida.
Muhammad Garba ya ce: “Za a fara bin gida-gida don gwajin ne daga karamar hukumar Nasarawa saboda itace tafi yawan masu wannan cuta a cikin kananan hukumomi 44 da jahar ke dasu. 
Kafin fara wannan gwaji, za a fara ba wa ma’aikatan kiwon lafiya horo na musamman a kan yadda za su gudanar da wannan gwaji na bin gida-gida”.
Domin Samun zafafan labaran da muke sakawa a FACEBOOK taba Na
Kwamishinan ya kara da cewa: “Idan aka fara gwajin gida-gidan a kananan hukumomin da cutar tafi yaduwa, to suma sauran kananan hukumomin jahar za a rinka tsintar wadanda za a yiwa gwajin,don ba za a barsu a baya ba”.
Wannan mataki da gwamnatin jahar ta dauka na zuwa ne kwanaki bayan gwamnatin ta bayar da umarnin bude kasuwanni da wuraren ibadu a ranakun Laraba da Jumma’a da kuma Lahadi bayan an shafe tsawon lokaci suna rufe saboda cutar korona.
Domin Samun zafafan labaran da muke sakawa a FACEBOOK taba Na

Leave a Reply

Your email address will not be published.