Dan majalisa ya yi barazanar barin aikinsa idan ba’a magance matsalar tsaro ba

Honarabul Victor Mela ya bukaci ‘Yan Majalisa su tashi tsaye domin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Victor Mela Dan zaria ya yi barazanar barin aikinsa a Majalisar Wakilai idan har ba’a ta kawa matsalar tsaro birki ba.
‘Dan Majlaisar na Billiri da Balanga ya ce dole ne a kawo karshen matsalar tsaro 
Mela ya bada wa’adin watanni biyu ga Majalisa ta tashi ta kare rayukan mutane.
 Honarabul Victor Mela mai wakiltar Balanga a Billiri a majalisar wakilan tarayyar Najeriya, ya koka da halin rashin tsaron da ake ciki, inda ya ce akwai bukatar ‘yan majalisa su tashi tsaye.
 Victor Mela ya bukaci ayi bincike game da kudin da ake kashewa bangaren tsaro.
 Mela ya zargi manyan jami’an tsaro da kar katar da dukiyar gwamnati wajen gina manyan gidaje. 
“‘Duk inda kaje, muddin ka ga gida mai kyau, to ko dai na kyaftin ne ko kuma na Sufeta ne.
Jami’an tsaron Najeriya ba sa yin abinda yakamata Kan yaki da Yan bindiga https://youtu.be/EVauMKSVUq4
 Mutane da-dama suna samun kudi da wannan harkar ta (rashin tsaro).” Inji ‘dan majalisar.
 Hon. Mela yake cewa “Lokaci ya yi da za mu tashi tsaye a matsayinmu na ‘yan majalisar tarayya, mu yi aikin da ya rataya a kanmu, na ganin cewa sha’anin tsaron kasa ya inganta.
 Da ya ke jawabi a ranar Alhamis data wuce, Mela ya yi barazanar barin majalisa, ya ce: “Ya shugaban majalisa da abokan aikina, ina so in fada cewa, zan ba kai na watanni biyu, idan wannan majalisa batayi wa ‘Yan Najeriya wani abin kirki dake nuna za a kawo karshen rashin tsaro ba, zan yi murabus.” “Kuma da gaske nake yin wannan magana. 
Yan bindiga na kashe mutane arana fiye da yadda korona ta kashe tunda tashigo -Hon. Gudaji kazaure
Ba za mu cigaba da zuwa nan, mu yi gum yayin da ake kashe jama’a ba. Abin ya yi yawa.” Ya tabbatar da cewa lallai da gaske yake yi. 
A karshe Victor Mela ya ce: “Dole mu nunawa ‘Yan Najeriya cewa mu ‘yan majalisa ne.” 
A nasa bangaren hon. Gudaji Kazaure ya yi Allah-wadai da yadda gwamnati ta karkata wajen yaki da ake yi da annobar COVID-19, ta manta da tsaro. 
Ban yarda da cutar korona ba, kuma baza ta kamani ba -Hon. Gudaji Kazaure

Leave a Reply

Your email address will not be published.