DCP Abba Kyari ya kama Masu safarar makamai suna siyarwa yan bindiga

A suma men da suka kaddamar Mai taken Operation Puff Adder Sarkin Yakin Nigeria DCP Abba Kyari babban kwamandan rundinar IGP Special Intelligence Response Team (IRT) sun  sami nasarar farautar gungun barayi masu fataucin miyagun makamai daga kasashen waje zuwa cikin gida Nigeria.
IRT sun kama 6,000 Rifles na Ak47 da Kuma wasu AK47 Rifles da Pistols, Wanda suke siyarwa ga Yan fashi da makami da Masu garkuwa da mutane da sauran Masu aikata muggan laifuka a Nageria.
Wadannan makaman anyi fasakwaurinsu ne, daga kasashen Libya da Burkina-Faso aka shigo dasu ta jam huriyar Kasar Benin zuwa Nigeria aka kai jihohin Katsina da Sokoto za’a sayarwa ‘yan bindiga, kafin DCP Abba Kyari ya samu nasarar kamasu
Haka Kuma Rundunar IGP-IRT da IGP-STS  sun kama Yan fashi da Masu garkuwa da mutane 38

Leave a Reply

Your email address will not be published.