Gwamnati ta ce ba’a sanya ranar da za’a bude makarantu ba

Gwamnati ta ce ba’a sanya ranar da za’a budewa makarantu ba.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa har yanzu bata sanya lokacin da makarantu za su sake budewa ba, wadan da aka kulle a yayin barkewar cutar Coronavirus a cikin kasar.
Dokta Osagie Ehanire, Ministan Lafiya ya ce makarantu za su sake buɗewa, lokacin da gwamnati ta sami damar tabbatar da daidai to a cikin tsaro da hana yaɗuwar cutar COVID-19 a duk faɗin ƙasar.
Saboda yan bindiga ya kamata ayi kulle ba saboda korona-Hon. Gudaji Kazaure
An hana bude Makarantu ne  da gudanar da taron ibada da kuma taron jama’a, watanni biyu da suka gabata daga Gwamnatin Tarayya sakamakon barkewar cutar Coronavirus.
Bayan watanni da rufewa, duk da haka, gwamnati ta sassauta dokar hana yin taro na addini tsawon makonni hudu yayin da makarantu za su kasance a rufe.
Ban yadda Akwai Korona ba, Kuma baza ta kamani ba.-Hon. Gudaji kazaure
Ehanire, yayin da yake jawabi ga manema labarai, yayin taron kwanaki 100 na aikin kwamitin shugaban kasa a kan cutar COVID-19 a Abuja, a karshen mako ya ce ba a sanya ranar da za a sake bude makarantu ba.
Ministan ya ce gwamnati za ta ci gabawa da sanya ido tare da nazarin yanayin cutar, kafun ta yanke hukunci lokacin da za a sake bude makarantu.
A cewar Ehanire: “Babu wani takamaiman ranar da za a koma makarantun.
Jami’an tsaron Najeriya ba sa yin abinda yakamata Kan yaki da Yan bindiga
A wata majiiyar mai ba shugaban kasa shawara kan cutar COVID-19 tana nazarin halin da ake ciki, tana yin nazari kowane mako biyu, zuwa hudu don tantance halin da ake ciki kuma, ta yanke hukuncin hilin da kasar take ciki da zarar an tabbatar da cewa kasar tayi lafiya za’a bude makarantu.
“Muna karfafawa makarantun hadin guiwa da su rungumi koyo ta kafafan yada labari, gidajen talabijin, rediyo, ko kuma ta internet kai tsaye, da kuma jajircewa wajen daukar ilimi kamar yadda ya kamata.
“Muddin aka tantance bayanai sannan aka auna hadarin yadawar cutar, sannan aka tabbatar da komai ya dai-dai ta, makarantu za su sake budewa.
“Gwamnatin Tarayya na matukar daukar matakan da suka dace don ganim hana yaɗuwar cutar, da kuma bude makarantu

Leave a Reply

Your email address will not be published.