Ganduje ya gana da kungiyar masu masana’antu MAN Kan yadda za’a farfado da tattalin arziki a kano
Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya gana da kungiyar masu masana’antu wato Manufacturers Association of Nigeria MAN, akan hanyoyi da gwamnati zata bi wajen ganin an farfado da tattalin arzikin jihar Kano musamman ganin illar da cutar Coronavirus wato Covid-19 tayi, na dakusar da al’amuran kasuwanci a jihar Kano dama ‘kasa baki daya.
Tawagar sunzo bisa Jagorancin Shugaban cibiyar ciniki da Masana’antu ta Jihar Kano Alh Dalhatu Abubakar Alhamsad inda sauran shugabannin duka suka tofa albarkacin bakinsu akan wannan mas’ala.