JUNE 12 Buhari ya ayyana ranar juma’a a matsayin ranar hutu domin bukukuwan Democracy Day

JUNE 12 Buhari ya ayyana ranar juma’a a matsayin ranar hutu domin bukukuwan Democracy Day

 Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da ranar Juma’a mai zuwa a matsayin ranar hutu ga yan Nigeria, domin su samu damar gudanar da bukukuwan Democracy Day, wanda Gwamnatinsa ta sauya daga 29 may zuwa June 12 domin tunawa da gwagwarmayar da Abiola yayi wajen samar da mulkin siyasa a Nigeriya.
Ministan al’amuran cikin gida Rauf Adesoji Aregbesola ne ya fitar da sanarwar wacce a cikinta ya nemi mutanen Nigeria suyi amfani da ranar June 12 wajen gudanar da addu’o’in godewa Allah sakamakon samar musu da Shugaba Buhari da yayi a matsayin shugaban Najeriya.
Ministan ya sanar da yan Nigeria dasu kasance masu amfani da tsarin tazara a yayin gudanar da shagul gulan ranar june 12

Leave a Reply

Your email address will not be published.