MANYAN ABUBUWAN TARIHI DA SUKA FARU A RAYUWAR MARIGAYI SANI ABACHA DA YA KAMATA KOWA YA SANI

MANYAN ABUBUWAN TARIHI DA SUKA FARU A RAYUWAR MARIGAYI SANI ABACHA DA YA KAMATA KOWA YA SANI

Yanzu Shekaru 20 kenan da mutuwar shugaban mulkin soja na Najeriya Sani Abacha
Har yanzu ra’ayoyin mutane sun bambanta a kan Marigayi Sani Abacha a Najeriya. 
Shugaba mai ci Muhammadu Buhari, wanda shi ma ya taba yin mulkin soja, ya yabe shi da cewa ya samar da ci gaba kamar gina tituna da bunkasa harkar ilimi da lafiya.
Amma wasu na zargin gwamnatinsa da yin kama-karya da take hakkin dan adam.
Jami’an tsaron Najeriya ba sa yin abinda yakamata Kan yaki da Yan bindiga https://youtu.be/EVauMKSVUq4
Ga dai wasu manya kuma muhimman abubuwa  dangane da rayuwar marigayi Sani Abacha:
A 20 ga watan Satumba 1943 aka  haifi Janar Sani Abacha a jihar Kano dake arewacin Najeriya.
Ya kammala makarantar horon aikin soji dake Kaduna a 1963, ya kuma samu karin horo a Birtaniya.
Yan bindiga na kashe mutane arana fiye da yadda korona ta kashe tunda tashigo -Hon. Gudaji kazaure
Ya auri Maryam Jiddah a shekarar 1965 sun haifi  ‘ya’ya 10 tare, amma babban cikinsu ya mutu.
A shekarar 1967 Abacha na daga cikin sojojin da suka yi yakin basasar Najeriya da aka yi da ‘yan awaren Biafra, kuma ya ci gaba da samun girma a soja.
A shekarar 1983 Abacha Ya yi fice sosai a Najeriya, saboda rawar da ya taka a juyin mulkin da aka yi wa gwamnatin Shugaba Shehu Shagari a ranar 31 ga watan Disamba. 
Bayan nan ne aka dora Janar Muhammadu Buhari a matsayin shugaban mulkin soja.
A 1985 ne ya taimaka aka hambarar da gwamnatin Janar Muhammadu Buhari da sa hannun sa.
 Ya kuma taimaka an dora Janar Ibrahim Babangida a mulkin kasar, shi kuma Abacha aka kara masa girma zuwa Manjo Janar.
Ban yarda da cutar korona ba, kuma baza ta kamani ba -Hon. Gudaji Kazaure
A 12 ga watan Yuni 1993 aka gudanar da zabe don mika mulki ga farar hula kamar yadda aka dade ana jira.
 A sakamakon farko-farko ya nuna cewa mashahurin mai kudin nan Moshood Abiola ke kan gaba, Janar Babangida ya soke sakamakon zaben.
A Agusta 1993 Aka nada Abacha Ministan Tsaro, bayan da Babangida ya sauka ya kuma samar da gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin Ernest Shonekan.
A 17 ga watan Nuwamba 1993 Shonekan yayi murabus ya kuma mika mulki ga Abacha, a wani al’amari da mafi yawan mutane ke ganin kamar wani juyin mulkin ne. 
Ana zargin mulkinsa na cike da cin zarafin bil’adam da take ‘yan cin fadin albarkacin baki.
A shekarar 1994 Moshood Abiola ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa saboda cin zaben da ‘ya ‘yi’ amma an kulle shi.
 
Mulkin Abacha ya fuskanci Allah-wadai daga kasashen turawa, dama  dakatar da Najeriya daga kungiyar kasashe renon Ingila, bayan da aka kashe masu kula da muhalli tara 9, daga yankin Ogoni, wadanda suke zanga-zangar adawa da ayyukan gwamnati da kamfanin mai na Shell. 
Daga cikinsu akwai Ken Saro-Wiwa, wani mai rubuta wake, wanda kuma aka zaba cikin wadanda za a bai wa lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel.
A shekarar 1996 Aka zabi Abacha a matsayin shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin kasashen Yankin Afirka Ta Yamma (Ecowas).
A shekarar 1998 Abacha ya tura dakarun Najeriya zuwa Saliyo a wani kokari na hambarar da gwamnatin mulkin soja da kuma dawo da gwamnatin farar hula wacce aka hambarar shekara guda kafin nan.
A irin wannan Rana ta 8 ga watan Yuni 1998 Abacha ya mutu sakamakon bugun zuciya da ake zargin shi ya yi sanadinsa, an kuma binne shi a wannan ranar.
 Shekara guda bayan nan ne Najeriya ta koma kan turbar dimukradiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.