Buhari ya mika wa Majalisar sunan Jastis Monica Dongban-Mensem a matsayin shugabar kotun dau kaka kara

Buhari ya mika wa Majalisar Dattawa sunan Jastis Monica Dongban-Mensem a matsayin shugabar kotun daukaka kara.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa majalisar dattawa, sunan Jastis Monica Dongban-Mensem, a matsayin sabuwar shugabar kotun daukaka kara domin tantancewa.

Bisa lamunin da kundin tsarin mulkin kasa ya bai wa shugaba Buhari, yana neman amincewar majalisar wajen nadin Jastis Monica, a matsayin sabuwar shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya.

Mai magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu ne, ya wallafa sanarwar hakan a kan shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 8 ga watan Yunin 2020.

Haka kuma shugaban kasar ya tabbatar da wannan sanarwa da kansa a sakon da wallafa kan shafinsa na dandalin sada zumunta na Twitter a Yammacin ranar Litinin.

Kamar yadda lamarin ya zamto al’ada, hukumar shari’ar kasa, ta shawarci shugaban kasa Buhari akan nadin Jastis Dongban-Mensem a matsayin sabuwar shugabar kotun daukaka kara a kasar.

A halin yanzu Jastis Dongban-Mensem babbar mai shari’a ce a kotun daukaka kara.

Hakazalika ita ce mai rikon kwarya ta shugabancin kotun daukaka kara ta kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.