Ganduje ya raba kayan kiwon Lafiya da kudin su yakai Naira Bilyan N1.052 Billion

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya kaddamar da rabon kayan asibiti
da kayan haihuwa  na Mata
da magunguna da kuma kayan kariya ga ma’aikatan lafiya wato PPEs da face masks da sauran su

wanda kudin su ya kama N1.052Billion ga asibitoci na kananen hukumomi guda 44 na jihar Kano. 


Kayyayyakin na hadin gwuiwa ne da Gwamnatin Jiha da kungiyoyin agaji na duniya da suka hada da MNCH2, UNICEF, USAID, SOML da kuma SDGs da maaikatar aiyuka ta taraiya.

Yayin da yake kaddamar da rabon kayan a wajen ajiyar kayayyakin lafiya na Rangaza dake karamar hukumar Ungoggo

Ganduje ya bukaci dukkan maaikatan lafiya dasu koma bakin aikin su ka’in da na’in su kuma guji rashin bawa marasa lafiya kulawa yayin aikin nasu.

Gwamna Ganduje na tare da mataimakin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna da Kwamishinan lafiya Dr Aminu Tsanyawa da sauran mayna jami’an maaikatar lafiya na jiha.

Leave a Reply

Your email address will not be published.