Zanga – zanga ta Rin cabe a Katsina Kan matsalar tsaro

Zanga – zanga ta Rin cabe a  Katsina Kan matsalar tsaro

Ayau Talata ne mazauna garin Yan tumaki a karamar hukumar Dan musa a jihar Katsina suka yi tururuwar fitowa kan tituna domin gudanar da zanga – zanga a kan halin rashin tsaro da suke fama dashi.

Zanga – zangar ta barke ne sakamakon sace wani ma’aikacin lafiya da diyarsa da wasu ‘yan bindiga sukayi.

Majalisa ta nemi a Kara daukar sojoji dubu Dari 100,000

Wata majiya ta shaidawa jaridar Premium Times cewa wasu ‘yan bindiga ne suka kaiwa ma’aikacin lafiyar, Mansir Yusuf, hari da misalin karfe 1:00 na dare tare da yin awon gaba dashi da diyarsa.

Garkuwa da ma’aikacin lafiyar da diyarsa na zuwa ne a cikin kasa da mako biyu da kai hari tare da kashe hakimin Yan tumaki, Atiku Abubakar, wanda ‘yan bindiga suka harbe a gidansa.

Jami’an tsaron Najeriya ba sa yin abinda yakamata Kan yaki da Yan bindiga- Gudaji Kazaure https://youtu.be/EVauMKSVUq4

Wata majiya da ta nemi a boye sunanta ta sanar da Premium Times cewa ma’aikacin lafiyar da aka sace makwabci ne ga hakimin da ‘yan bindiga suka kashe.

Masu zanga – zangar, yawancinsu matasane, da kananan yara, sun rufe manyan hanyoyi, tare da sukar gwamnati a kan nuna halin ‘ko in kula’ tun bayan kisan hakimin garin.

“Har yanzu babu wani jami’in tsaro a garin tun bayan kisan hakimi. 

Yan bindiga na kashe mutane arana fiye da yadda korona ta kashe tunda tashigo -Hon. Gudaji kazaure

Sun ce suna yin zanga – zanga ne domin jan hankalin gwamnati kafin wadannan ‘yan bindigar su fara kawo musua hari a kowace rana.

Leave a Reply

Your email address will not be published.