Gwamna Zulum ya tabbatar da mutuwar mutane 81 da bace war mutane 6 a harin da Yan bindiga suka Kai borno

Gwmna Zulum ya tabbatar da cewa Mayakan Boko Haram sun kashe mutune 81 ya yinda  suka jikkata 8 da sace mutane  13, a jihar Borno, kwana biyu bayan Babban Hafsan Mayakan sojin Kasa Tukur Buratai ya bar jihar, yaje  yiwa Buhari tilawar nasarar kashe Mayakan Boko Haram 1429 da kame 116.
Wanda ya tsallake rijiya da baya ya shaidawa Gwamna Zulum cewa Maharan sun shafe awa biyu suna cin karensu babu babbaka da tsakar rana a kauyen Foduma Kolomaiya dake Karamar Hukumar Gubio.
Bayan mutane 81 da suka kashe, rahotanni sun ce maharan sun kashe kimanin shanu 300 kuma suka sace kimanin 1,000.

Majiyarmu ta ce harin na ranar Talata ya zo ne kwana guda bayan ‘yan Boko Haram sun tare matafiya a kan babban titin Monguno, inda suka jikkata mutane da dama.
Daya daga cikin majiyoyin ya ce akwai mutane da dama da aka nema aka rasa bayan harin, wanda mutane da yawa sun jikkata.
Dukkan kokarin da aka yi na ji ta bakin mai magana da yawun rundunar sojoji, kanar Sagir Musa ya ci tura.
Bai daga wayarsa ba, kuma bai amsa sakon kar ta kwana da aka aike masa ba har zuwa  karfe 10.09 na daren jiya talata.
Duk da haka jami’ai a wata babbar hukumar kasashen duniya dake aiki a jihar Borno da ‘yan sintiri sun tabbatar da harin na Gubio.
“Shi ne hari mafi muni a ‘yan kwanan nan. Nisan kauyen ya sa ba za a iya kai musu agaji ba a kan kari”, inji jami’in.
“Sun kashe mutane da yawa wasu kuma sun bace kasancewar da tsakar rana suka kai harin”, inji wani jami’in.
Dan sintirin ya ce sun kirga gawa 69. “Ba cin wadanda ba a gani ba, inda yace Zuwa gobe (yau laraba kenan) za a iya samu karin bayani a kan harin”, inji shi.
Bayan Gwamna Zulum ya kai ziyara garin an tabbatar wa gwamnan cewa, mutane 81 ne suka mutu, 13 suka jikkata, sannan aka sace mutane 8
Janar Tukur Buratai ya bar jihar Borno ranar Lahadi ya ce sojoji na samun gagarumar nasara a yaki da suke ci gaba da yi da kungiyar Boko Haram.

A jawabinsa ga Shugaba Buhari a Abuja ranar Litinin, Buratai ya ce a tsawon zamansa sojoji sun kashe ‘yan Boko Haram 1,429, sannan suka kame wasu 116.

Leave a Reply

Your email address will not be published.