Gwamna Zulum ya tabbatar da mutuwar mutane 81 da jikkata mutane 13 da sace mutane 8

Gwamnan jihar Borno, Baba gana Umara Zulum, ya ziyarci ƙauyen Faduma Kolomdi na makiyaya dake yankin ƙaramar hukumar Gubio na jihar Borno.

A ƙauyen ne dai aka kai wani hari inda ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne a jiya Talata inda suka kashe mutanen ƙauyen 81, suka raunata mutune 13, kuma suka sace mutune 8, ciki kuwa har da mai garin ƙauyen.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Isa Gusau ya fitar, gwamnan jihar ya yi kira ga sojojin Najeriya da suyi wani gagarumin kukan kura, wanda zai kawo ƙarshen masu tayar da ƙayar baya a yankin tafki Cadi.
Wani wanda ya tsallake rijiya da baya yayin harin, ya shaida wa gwamnan jihar cewa masu tayar da ƙayar bayan sun isa ƙauyen ne da misalin karfe goma na safiyar jiya Talata, da manyan bindigogi da motocin sulke na yaƙi.

Maharan sun kwashe tsawon sa’o’i shida suna ƙaddamar da hari, kafin su bar kauyen da misalin karfe hudu na yamma.

Leave a Reply

Your email address will not be published.