Rikici Ya Barke Tsakanin Asari Dokubu sugaban kungiyar Niger delta da Nmandi Kanu Shugaban Rajin kafa yankin Biafra

Rikici Ya Barke Tsakanin Asari Dokubu  da Nmandi Kanu Shugaban Rajin kafa yankin Biafra

Kazamin Rikicin Ya Barke tsakanin Shugaban IPOB Mazi Nmandi Kanu wanda kuma shine Jagoran Kafa Biafra a Najeriya da Shugaban Kungiyar Niger Delta Volunteers Force, Alhaji Mujaheed Dokubo Asari, inda Shi Nmandi Kanu ya riya cewa Mujaheed Asari ya Damfare shi Miliyan 20, yayin daya roke shi Miliyan 200 da zummar cewa kafin ya dawo Najeriya zasu kafa kasar Biafra.
A dalilin haka ne aka dinga samun cacan baki tsakanin Shugabanni Guda biyu inda kowa yake zargin dan’uwansa da Yaudara.
A Bidiyon da Mujaheed Asari ya fitar ya rantse da Alqur’ani mai Girma cewa Nmandi Kanu bai bashi komai ba, inda yace idan yana da Gaskiya ya nuna wa Duniya wani dalili akan haka.
Daga Karshe Mujaheed Asari Dokubo ya bayyana Nmandi Kanu a Matsayin Mutum mayaudari mai neman jefa Jama’arsa cikin masifa batare daya waiwayesu ba.
Asari Dokubo ya kara da cewa akwai Yaran IPOB dayawa a hannun Yan Sanda da Jami’an DSS amma Nmandi Kanu bai taba waiwayarsu ba.
Yanzu Haka dai Yawancin Matasa yan Kabilar Igbo Suna kan bayyana ra’ayin su a kafafen Sadarwa inda suka nuna Rashin Amincewar su ga Shugabanni guda biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.