Sau takwas akayi yun kurin yiwa Abacha juyin mulki

Tsohon jami’in tsaron dake kula da tsohon shugaban kasa Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha,ya ce sau takwas ana yunkurin kifar da gwamnatin Abacha, amma mutane labarin juyin mulki uku kurum su ka sani. “Har lokacin da Abacha ya mutu, wasu na kitsa masa juyin mulki.”

 Haka kuma Hamza Al-Mustapha ya yi fashin baki game da dukiyar da ake cewa Abacha ya sace

 A cikin jawabansa, na kokarin kare mai gidansa game da zargin da ake yi masa na satar dukiyar gwamnati.

Hamza Al-Mustapha ya ce gwamnatin Sani Abacha ta tuntubi sarakunan Arewa dana Kudu da duk wasu manya da ake ji dasu a Najeriya, kafin gwamnati ta boye biliyoyin kudin da yanzu ake kira ‘satar Abacha.’

Al-Mustapha ya bayyana haka ne a lokacin da ya zanta da gidan rediyon BBC Hausa, inda ya ce dole tasa Janar Sani Abacha ya rika boye biliyoyin kudi a kasar waje domin  hararo cewa za a makawa Najeriya takunkumi.

“A dalilin wannan takunkumi ne Abacha ya boye kudin kasar a ketare saboda kada ‘yan Najeriya su shiga cikin matsala.”

Manyan abubuwan tarihi da suka faru a rayuwar San Abacha

https://www.arewagist.com.ng/2020/06/muhimman-abubuwan-da-suka-faru-rayuwar.html?m=1

Game da wannan kudi da ake maganarsu a yau, Hamza Al-Mustapha ya ce: “Mun tara Sarakunan Arewa da na Kudu, tare da manyan dake cikin gwamnati da wadanda ba su ciki a wancan lokaci.”

“Shawara ce wadda aka dauka bayan an yi taron masu ruwa da tsaki da sarakunan gargajiya na fadin Najeriya.”

Al-Mustapha ya ke cewa: “Ina fadan wannan ne saboda abin da na sani da kuma amana ga ‘yan Najeriya.”

Mun hadu ne a wani wuri da ake kira Camp Bassey officer’s mess a fadar shugaban kasa. A nan ne muka tattauna game da barazanar makawa Najeriya takunkumi, aka cim ma matakai da dama.”

“Ministan kudi, da ministan tsare-tsaren kasafin kudi da irinsu gwamnan babban bankin kasa na CBN sun halarci wannan taro.”

Dogarin na marigayi Sani Abacha yake cewa akwai ban mamaki a rika cewa wannan kudi na Abacha ne bayan babu hujjar dake nuna sa hannunsa, ko hotonsa a bankunan da aka ajiye kudin.

“ yace ina mamakin yadda ake cin zarafin Abacha.”

“Lokacin da ya karbi mulki, kudin kasar wajen Najeriya bai kai dala biliyan biyu ba, abubuwa babu tsari.”

Yace: “A shekara hudu da watanni takwas, kudin suka  koma Dala biliyan tara.”

“Watanni tara da mutuwar Abacha wannan kudi sukabi iska. Har yau wadanda suka sace wannan kudi suna nan, babu yadda akayi dasu.”

Sojan ya ce sau takwas ana yunkurin kifar da gwamnatin Abacha, amma mutane labarin juyin mulki uku kurum su ka sani. “Har lokacin da Abacha ya mutu, wasu na kitsa masa juyin mulki.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.