Yan bindiga sun kashe mai garin Mazoji a Matazu tare da kashe mutune 3 a Yankara

A daren jiya Yan ta’adda sun kashe mai garin Mazoji a Matazu tare da kashe mutune 3 a Yankara

Katsina Daily Post News ta sami labarin kashe mai garin Mazoji Dikko Usman, a karamar hukumar Matazun jihar Katsina sakamakon harin yan bindiga.
Anyi zanga-zanga a katsina saboda matsalar tsaro
Haka Kuma Mahara sun kai hari a karamar hukumar Faskari, inda basu sami damar shiga garin ba, amma sun kashe mutune 3 a yankin Yankara.
Jihar Katsina na cikin kalubalen harin yan ta’adda sosai, musamman a yankin Danmusa, Batsari, Safana, Jibiya, Faskari, Sabuwa, Matazu, Dandume, da sauran kauyuka da garuruwan jihar Katsina da daka.
Masu zanga-zangar Rashin tsaro a katsina sun Nuna fushinsa 
Allah Ya kawo wa jihar Katsina dauki a kan wadannan miyagun yan ta’adda amin

Leave a Reply

Your email address will not be published.