Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Tara A Kauyukan Karamar Hukumar Faskarin Jihar Katsina

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Tara A Kauyukan Karamar Hukumar Faskarin Jihar Katsina

Haka Kuma sun kashe Mai garin Mazoji A Karamar Hukumar Matazu
sun sace mata 12 A kauyukan Faskari
A daren jiya Juma’a, yan bindiga bisa babura dauke da bindigogi, sun kara kai tagawayen hare-hare a wasu kauyukan karamar hukumar Faskari, inda aka tabbatar sun kashe mutum tara da kuma sace Mata goma sha biyu.
Anyi zanga-zanga a katsina saboda matsalar tsaro
Wani Mazaunin garin ya tabbatar wa RARIYA cewa a daren jiya yan bindiga sun yi yinkurin shigowa karamar hukumar Faskari, Amma sun samu turjiya daga sojoji da kuma Yan sa kai na garin Faskari. 
Amma sun shiga garin Yankara, sun kashe mutum Ukku sun kuma sace Mata ukku. 
Kuma sun shiga garin Unguwar Kafa inda suka kashe mutum Ukku. 
Masu zanga-zangar Rashin tsaro a katsina sun Nuna fushinsa 
Haka Kuma sun shiga garin Fankama sun kashe mutum daya sun tafi da Mata ukku, sun kuma balle sama da shagunan goma na garin. 
A daren jiyan sun shiga garin Dogan Dawa sun kashe mutum daya kuma sun sace Mata guda biyu. 
Haka kuma sun shiga garin Hayin Yahuza sun sace mutum daya, sun kone mota daya. 
Sun kuma shiga garin Sabon Layi, duk a karamar hukumar Faskari sun sace Mata ukku duk a daren jiya Juma’a.
Duk a daren jiya, ‘yan bindigar sun shigo garin Mazoji, a Karamar Hukumar Matazu, inda suka kashe Maigarin Mazoji har lahira. 
Sarkin Fulani Fafu, Alhaji Dikko Usman, sun zo ne da Misalin karfe biyu na daren jiya, a gidansa suka kuma kashe shi har lahira.
2 hrs · Facebook for Andr

Leave a Reply

Your email address will not be published.