Yan sandan sun karbi rahotan yiwa Mata 717 fyad’e cikin watanni 5 a Nigeria

Yan sanda sun Sami rahotan yiwa mata 717 fyade cikin watanni 5 a Najeriyay – IGP  

 Sifeta Janar din ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya ce matsalar fyade 717 suka samu a cikin watanni biyar na farkon 2020. 
A yayin zantawa da manema labarai bayan ganawar da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari, Lai Mohammed, ministan yada labarai da al’adu tare da Paullen Tallen, ministar harkokin mata, Adamu ya ce mutum 799 suka cafke zuwa yanzu.
 A cikin makonni kadan da suka gabata, lamarin fyade ya kasance babbar matsalar da ta addabi Najeriya kuma ake ta tattaunawa a kai.
 ‘Yan Najeriya na ta magana a kan ladabtar da masu laifin. 
IGP ya ce sun kai 631 daga ciki gaban kuliya yayin da ake ci gaba da bincike a kan mutum 52 kuma ana gab da kammalawa. 
“Masu tabbatar da an bi doka suna kan wannan matsalar. A mafi yawa daga cikin matsalolin, jama’a basu san matakin da jami’an tsaro ke dauka ba,” yace.
 “Yan sandan Najeriya sun samu matsalar fyade da aka kai gabansu har 717 daga watan Janairu zuwa Mayu a fadin kasar nan.
 613 daga ciki an kammala bincike yayin da wasu ake kan bincikarsu. 
“Yan sandan da sauran jami’an tsaro tare da kungiyoyin taimakon kai da kai na hada kai don ganin karshen cin zarafin jinsi.
 “NGO da CSO suna da karfin iya shawo kan irin wadannan laifukan. 
Gwamnati ta matukar damuwa da wannan al’amarin kuma tana son saka mataki mai tsauri.
” Yayin da yake bayyana fyade a matsayin rashin imani, Adamu ya bukaci ‘yan kasa da su hanzarta kai rahoton duk wani abu da ya danganci cin zarafin jinsi.
 “Akwai dalilai da yawa da suke sa ake yi. 
Wasu mazan saboda tsafi suke yi, wasu kuma saboda ‘yan gida suka samu. Amma bai kamata a barsu haka ba,” yace. 
“Ina sanar daku cewa gwamnati na yin kokari a kan hakan kuma za ku ganni tare da ministan yada labarai da kuma ministar harkokin mata, Pauline Tallen.
 “Daga yanzu, ba cikin kasar nan ba kadai, har da kasashen ketare za mu hada kai don yakar fyade.” 

Leave a Reply

Your email address will not be published.