Gwamna Masari na ganawar sirri da manyan shugabannin jami’an tsaron kasa.
Mun samu labarin cewa yanzun haka gwamna Masari na ganawar sirri da manyan jami’an tsaron Nijeriya a fadar gidan gwamnatin jihar Katsina.
Daga cikin jami’an tsaron da aka hango a gidan gwamnatin sun hada shugaban yan sandan Nijeriya , da kuma na farin kaya DSS, gami da kuma mai ba shugaban kasa shawara a fannin tsaro Babagana Manguno.