GWAMNATIN JIGAWA ZATA RUFE KASUWANNIN DA BASU BI KA’IDAR KARIYA DA KORONA BA

GWAMNATIN JIGAWA ZATA RUFE KASUWANNIN DA BASU BI KA’IDAR KARIYA DA KORONA BA

Gwamnatin jihar Jigawa ta nuna damuwa kan yadda mutane basa kiyaye ka’idojin hana kamuwa da cutar covid-19 a kasuwanni.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ne ya sanar da hakan a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a gidan gwamnati.

Ya ce an sake bude kasuwannin ne domin ci gaba da harkokin saye da sayarwa sakamakon raguwar yaduwar cutar a jiahr, amma abin takaici alumma basa kiyayewa da dokokin da aka shimfida.

Gwamnan ya yi gargadin cewar gwamati zata rufe duk wata kasuwa da aka samu mutane basa kiyayewa da dokokin yaki da kamuwa da cutar.

Ya kuma bada umarnin cire shingayen duba ababan hawa dake kan iyakokin jihar nan.

Inda kuma ya yabawa jami’an tsaro da sauran alummar jihar, bisa hadin kai da goyan bayan da suka bayar  lokacin sanya dokar kulle wadda ta haifar da da mai idanu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.