Yau Likitoci sun janye yajin aikin Sai baba ta gani bayan ganawa da kungiyar gwamnonin Najeriya

Yau Likitoci sun  janye yajin aikin Sai baba ta gani bayan ganawa da kungiyar gwamnonin Najeriya

Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta tsoma baki cikin rashin jituwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyar Manyan Likitocin Najeriya NARD da har ta kai ga shigarsu yajin aiki.

Shugaban sashen hulda da al’umma na kungiyar gwamnonin, Abdulrazaque Bello-Barkindo, shi ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis cikin birnin Abuja.

A sanarwar da Barkindo ya fitar, ya ce kungiyar gwamnonin ta gana da fusatattun Likitocin, sun kuma nuna amincewar su domin sulhunta lamarin.

Likitocin yayin bayyana fushinsu ga kungiyar gwamnonin, sun kuma ba da tabbacin su janye yajin aikin ayau litinin. 

An rawaito cewa, dukkanin manyan kungiyar likitocin ta NARD sun hallara a sakateriyar NGF inda suka gana da shugaban NGF, Kayode Fayemi, gwamnan jihar Ekiti.

Daga bisani kungiyar likitocin a gaban Darakta Janar na NGF, Asinshana Bayo Okauru, sun kuma gana da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, inda shi ma suka bayyana masa fushinsu.

Wannan shi ne karo na farko da kungiyar likitocin takai kukanta har gaban kungiyar gwamnonin kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

Gwamna Fayemi ya yaba ma likitocin kan yadda suka ci gaba da zama a kasarsu domin yin hidima duk da tarin alheri da kuma tayin da suke samu daga kasashen waje.

Sai dai Gwamnan ya tunatar dasu cewa tserewa daga kasarsu ba tare da yi mata hidima ba, zai zama butulci ga gwamnatin kasar da tayi ruwa da tsaki wajen ganin sun kware a kan aikinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.