Gwamna Zulum ya dauki manoma 6,111 aiki a Borno

Gwamna Zulum ya dauki manoma 6,111 aiki a Borno

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya dauki manoma 6,111 a shirin manoma na kananan hukumomi 10 na jihar.

– Kwamishinan aikin gona na jihar, Bukar Talba ne, ya bayyana hakan a jawabin da yayi wa manema labarai a Maiduguri.


– Talba ya ce, sakamakon aikin ‘yan ta’adda, akwai yiwuwar tabar-barewar tsaron abinci a jihar.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya dauki manoma 6,111 aiki a babban shirin manoma a fadin kananan hukumomi 10 na jihar don hana rashin abinci a nan gaba.

Kwamishinan aikin gona, Bukar Talba, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da aka yi dashi a Maiduguri a ranar Litinin, 22 ga watan Yuni, wanda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin jihar Borno ta kafa kwamitin don kafa shirin inganta noma da samar da abinci a jihar.

Kamar yadda Talba yace, sabbin manoman za su yi aiki don fadada ayyukan samar da abinci. 

Za suyi aiki da mafarauta da kuma jami’an tsaron farar hula yayin da suke gonakin.

Ya ce sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda, an samu karancin manoma domin wasu sun yi gudun hijira, kuma hakan babbar barazana ne ga tsaron abinci a jihar.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar na kokarin habbaka tattalin arzikin jihar ta hanyar bada fifiko a bangaren noma da kiwo.

A wani bangare, a kokarin gwamnatin jihar na yakar ayyukan ‘yan ta’adda, Gwamna Babagana Umaru Zulum ya kwace gidaje 100 da aka gina a garin Bama.

Gwamnan ya bada gidajen a ranar Litinin 8 ga watan Yuni ga ‘yan gudun hijira a karamar hukumar Bama.

Leave a Reply

Your email address will not be published.