Buhari ya Ayyana Giadom a matsayin shugaban riko na jam’iyyar APC

Buhari ya Ayyana Giadom a matsayin shugaban riko na jam’iyyar APC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce Victor Giadom ne shugaban riko na jam’iyyar APC na kasar.
Mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai Garba Shehu ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter ranar Laraba da yamma.
Ya ce shugaban ya dauki wannan mataki ne sakamakon shawarwarin masana shari’a kan halin da jam’iyyar take ciki.
Sanarwar ta ce Shugaba Buhari zai halarci taron da Victor Giadom ya kira ranar Alhamis, wanda za a gudanar ta bidiyo, tare da sa ran cewa gwamnonin jam’iyyar da shugabannin majalisar dokoki na APC za su halarci taron.
Sanarwar ta fadar shugaban kasa ta yi kira ga kafofin watsa labarai su guji yada rikice-rikicen da ake yada cewa jam’iyyar APC ta na da su, sannan su kiyayi ba da dama ga mutane suna fadar son ransu kan lamarin shugabancin jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.