An Kama Mutane 40 Da Laifin Yi Wa Yara Fyade Da Luwadi A Jihar Katsina

An Kama Mutane 40 Da Laifin Yi Wa Yara Fyade Da Luwadi A Jihar Katsina


   Za mu tabbatar an hunkunta su kamar yadda dokar kasa ta tanada, Cewar kwamishinan ‘yan sanda.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, karkashin jagorancin kwamishinan Yan Sanda Alhaji Sanusi Buba ta yi nasarar cafke wadanda ake zargi da yi wa kananan Yara fyade da kuma luwadi har su sama da arba’in, daga watan Aprilu zuwa watan Yuni na wannan shekarar da muke ciki.
Kwamishinan ‘yan sanda, Sanusi Buba, wanda ya samu wakilcin Kakakin rundunar ‘yan sanda SP Gambo Isa, a lokacin da yake holen masu laifin a helkwatar rundunar da ke Katsina.
Wadanda aka kamo masu aikata lalata da  kananan Yara maza da mata, an kamo su daga kananan hukumomi talatin da hudu na jihar Katsina. 
 Akwai masu mabanbanta shekaru acikin Masu laifin. Akwai masu shekaru ashirin zuwa sittin da biyar. 
Akwai wanda ya yiwa kanwarsa fyade wanda suke uba daya. 
Akwai kuma wadanda suke da wani rukuni, wanda kowa sai ya yi lalata da Yaran da suka samu.
 Akwai wani Mai waka yabo, da ake zargi da dauko wani yaro daga garin su Abukur, ya kawo shi cikin garin Katsina, yana lalata da shi ta Dubuta. 
Akwai dan shekara ashirin da ya yiwa yar shekara biyar fyade. Duk a cikin su akwai dan shekara sittin da biyar da ya lalata kananan yara guda ukku. 

Mafi yawancinsu sun amsa laifukkan su.

Kwamishinan ya ce da zaran an kammala bincike za a maka su gaban kuliya manta sabo, wasu kuma tuni an fara gurfanar da su gaban kotu.
Haka Kuma ya yi kira ga iyaye su dunga kula da suwa yayansu ke mu’amala ta yau da kullum.

Leave a Reply

Your email address will not be published.