Muhimman Abubuwan da aka zatar a taron NEC na APC da Buhari ya jahoranta

Buhari ya Rushe Kwamitin Zartarwa na APC ya  nada Gwamnan Yobe Mai Mala Buni shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC

Muhimman Abubuwan da aka zartar a taron NEC na APC da Buhari ya jahoranta

An nada gwamnan jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya Mai Mala Buni shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC.
Kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar ne ya dauki wannan mataki bayan da ya soke kwamitin rikon APC din a wani taro da ya gudanar a ranar Alhamis da rana.
Hakan ya biyo bayan shawarwarin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar ne, kamar yadda mai taimaka masa kan shufakan sada zumunta Bashir Ahmed ya fada a shafinsa na Twitter.
An gudanar da taron ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja, kuma Shugaba Buharin ne ya jagoranci taron.
Mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajoda gwamnaonin jihohi na jam’iyyar APC da mambobin Kwamitin gudanarwarta su ma sun halarci taron ta allon talabijin ta intanet.
Ga dai wasu muhimman abubuwa da aka zartar a taron:
An Umartaci duka ‘yan jam’iyya da suka kai kara su janye kararraki
Haka Kuma an Amince da zaben fitar da gwani na jihar Edo
An Rushe Rushe kwamitin zartarwa na APC da nada Mai Mala Buni ya jagoranci kwamitin mutum 13 har tsawon wata shida.
Dama dai tun da farko wani ɓangare na jam’iyyar APCn ya ce taron da Shugaba Buhari ya jagoranta na ”ɓangaren Victor Giadom” a yau, haramtacce ne.
Sanarwar da shugaban APC na riko Mr Ntufam Hilliard Etagbo Eta da Sakataren riko Waziri Bulama suka sanya wa hannu ranar Laraba da almuru ta bayyana cewa “yaudarar” shugaban kasar aka yi ya amince cewa Mr Giadom ne sabon shugaban riko na jam’iyyar.
“Muna so mu bayyana ƙarara cewa mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa sun yi amannar cewa an bai a shugaban kasa gurguwar shawara ko kuma an yaudare shi ya amince da haramtaccen taron da wani mai suna Victor Giadom ya kira ranar 25 ga watan Yuni, 2020,” in ji sanarwar.
Ranar Laraba ne Shugaba Buhari ya ce Victor Giadom ne shugaban riko na jam’iyyar APC na kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.