Sirikin ganduje Tsohon gwamnan jihar Oyo Isiaka Abiola Ajimobi ya rasu

Tsohon gwamnan jihar Oyo Isiaka Abiola Ajimobi ya rasu a yau Alhamis bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Wani makusancin marigayin ne ya tabbatar wa BBC labarin rasuwar tasa.
Rahotanni sun ce tsohon gwaman ya rasu ne a wani asibiti da ke Legas.
Tun a makon da ya gabata ne dai aka yi ta raɗe-raɗin cewar Ajimobi ya rasu.
Kafin rasuwarsa, ya jagoranci jihar Oyo a matsayin gwamna tun daga 2011 zuwa 2019

Leave a Reply

Your email address will not be published.