Wani ɓangare na APCn ya ce taron da Buhari ya jagoranta na ”ɓangaren Victor Giadom” a yau, haramtacce ne.

Wani ɓangare na jam’iyyar APCn ya ce taron da Shugaba Buhari ya jagoranta na ”ɓangaren Victor Giadom” a yau, haramtacce ne.

Sanarwar da shugaban APC na riko Mr Ntufam Hilliard Etagbo Eta da Sakataren riko Waziri Bulama suka sanya wa hannu ranar Laraba da almuru ta bayyana cewa “yaudarar” shugaban kasar aka yi ya amince cewa Mr Giadom ne sabon shugaban riko na jam’iyyar.
“Muna so mu bayyana ƙarara cewa mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa sun yi amannar cewa an bai a shugaban kasa gurguwar shawara ko kuma an yaudare shi ya amince da haramtaccen taron da wani mai suna Victor Giadom ya kira ranar 25 ga watan Yuni, 2020,” in ji sanarwar.
Ranar Laraba ne Shugaba Buhari ya ce Victor Giadom ne shugaban riko na jam’iyyar APC na kasar, Wanda shi Kuma ya Kira taron jam’iyyar na kasa a ranar Alhamis.
A taron ne Buhari ya sanar da Rushe Kwamitin Zartarwa na APC inda ya  nada Gwamnan Yobe Mai Mala Buni shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC

Leave a Reply

Your email address will not be published.