Wani kamfanin shinkafa a Kano ya tirsa sawa Ma’aikata 600 Zama cikin Kamfanin Babu fita na tsawon wata uku 3

 Wani kamfanin shinkafa a Kano ya tirsa sawa Ma’aikata 600 Zama cikin Kamfanin Babu fita na tsawon wata uku 3

Yan sanda sun ceto leburori 600 da aka garkame tsawon wata uku a wata masana’antar Shinkafa a Kano

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta bada sanarwar ceto wasu leburori 600 da aka kulle a wata masana’antar shinkafa tsawon wata uku.
An kulle leburorin ne tsawon watanni uku a gona ko masana’antar da akafi sani da ‘Popular Rice Farm’.
Wasu da suka zanta da PREMIUM TIMES, sun ce an yi musu barazanar cewa duk wanda ya kuskura ya tafi gida domin ganin iyalin sa a lokacin Coronavirus, to zai rasa aikin sa.
Jami’an ‘yan sanda sun samu sammacin umarni daga kotu, inda suka banka cikin gonar ko masana’antar, suka kamo manajojin ta hudu, kuma suka fito da dukkan leburorin.
Leburorin sun shaida cewa an hana su ko da fita waje, gudun kada su kwashi cutar Coronavirus su watsa a masana’antar.
Daya daga cikin leburorin ya shaida wa manema labarai cewa rabon sa da waje tun a ranar 23 Ga Maris.
Wani mai suna Haruna Salihu cewa ya yi tun a ranar 28 Ga Maris yake a ciki a kulle suna aiki.
“Iyalan mu da iyayen mu basu san halin da mu ke ciki ba. Mata ta ta sha zuwa bakin kofa domin ta gan ni, amma ba a bari na fita.” Inji shi.
Shi ma wani direba mai suna Hashimu da yake jigilar samfarerar shinkafa daga Kebbi, ya bada labarin yadda aka kulle shi tsawon kwanaki uku, aka hana shi fitowa.
“Ni daga Yawurin Jihar Kebbi na kawo lodin samfarerar shinkafa. Yau kwana na uku, amma masu gadi sun kulle kofa sun hana ni fita. Ina son fita domin na mika wa yaro na kudin sayen abinci, amma an hana ni.
“Akwai ma wani aboki na da ya turo min naira 10,000, amma an hana ni zuwa banki na ciro kudin.” Inji Hashimu, wanda ya ce har yanzu jira ya ke yi a sauke masa lodin shinkafar domin ya koma, amma ba a sallame shi ba.
Yayin da kakakin ‘yan sandan Kano ya ce za a kammala bincike, a tura manajojin da aka kama su hudu kotu, shi kuwa babban manajan mai suna Abdulkarim, ya bada hakurin abin da ya faru, inda ya ce ba da sanin sa lamarin ya faru ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.