An kama Mutune 9,444 da laifukan shan kwayoyi da dangoginsu a Najeriya a 2019

Shan miyagun kwayoyi ya karu sakamakon zaman gidan da aka yi a lokacin dokar kullen COVID-19, a cewar Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA).

NDLEA ta ce shan kwayoyi ba bisa ka’ida ba ya karu ta yadda masu shan miyagun kwayoyi suka yi ta harhadawa tare da kirkirar kayan maye iri-iri a tsawon lokacin kullen.
Shugaban hukumar, Muhammad Mustapha Abdallah, ya sanar da haka a ganawarsa da ‘yan jarida ta fasashar zamani, yayin bikin zagayowar Ranar Yaki da Ta’ammuli da Kwayoyi da Safarar Dan Adam ta Duniya ta shekarar 2020.
Mutum 9,444 ne aka kama da laifukan shan kwayoyi da dangoginsu a Najeriya a 2019. Daga cikinsu kotu ta hukunta 1,195, wasu 795 kuma aka ba su shawarwari, kamar yadda ya bayyana.
“Yananin COVID-19 ya sa masu dogaro da kwayoyi kara shiga hadari domin dama can ba cikakkiyar lafiya garesu ba, al’umma na tsangwamarsu sannan babu halin samun kula da lafiya.
Abin da ya kara tsananta lamarin fiye da komai a yanzu shi ne matsin COVID-19”, inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.