Ganduje ya bada umarnin yi wa masu mukami a gwamnatinsa gwajin miyagun kwayoyi

Ganduje ya bada umarnin yi wa masu mukami a gwamnatinsa gwajin miyagun kwayoyi

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ana shirin yi wa duk masu rike da mukaman siyasa, ma’aikatan gwamnati da dalibai gwajin dole na miyagun kwayoyi a kano.
A wata takarda da kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba, ya fitar ranar Juma’a ranar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta duniya, ya ce za a fara gwajin dole daga cibiyar kula da magunguna.
Gwamnatin Ganduje na kokarin ganin ta yaki safara tare da ta’ammali da miyagun kwayoyi. Saboda haka ne ta kafa kwamitin yaki da hakan a jihar.
“Gwamnan ya samar da shirye-shirye da za su tabbatar da an shawo kan matasalar amfani da miyagun kwayoyi.
“Wannan ya hada da kafa kwamitin yaki da hakan wanda yake kamawa tare da kwace miyagun kwayoyin miliyoyin naira,” yace.
Ya yi kira ga jama’a da a dage wurin wayar da kan matasa a kafafen sada zumuntar zamani don su gane haduran da ke tattare da ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Su gane cewa hakan na da matukar hatsari ga rayuwarsu tare da tattalin arzikin kasar nan baki daya.
Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa, majalisar dinkin duniya ta ware ranar 26 ga watan Yuni a matsayin ranar yaki da ta’ammali da miyagu kwayoyi da safararsu a fadin duniya.
An ware tane don bayyana kokarinta wurin cimma manufar al’umma na yakar ta’ammali da miyagun kwayoyi.
A wannan ranar ta shekarar nan, ana kokari wurin wayar da kai, tare da ilmantar da jama’a don su gane matsalolin kwayoyi ga al’umma baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.