An Yi Jana izar sanata Ajimobi tsohon gwamnan Oyo

A ranar Alhamis ne Sanata Abiola Ajimobi ya rasu bayan fama da rashin lafiya.

Sanata Ajimobi wanda ya yi gwamnan Oyo na tsawon shekara takwas ya rasu yana da shekara 70 a duniya.
Ba a bar mutane da yawa sun halarci wajen jana’izar ba 
Da misalin karfe 12 na rana ne aka yi jana’izar Ishaq Abiola Ajimobi a Oke-Ado, kuma an gudanar da jana’izar ne a takaice da mutanen da basu fi 20 ba.
An sanya tsattsauran tsaro a yankin unguwar da gidan mamacin yake saboda masu son halartar jana’izar.
Cikin wadanda suka halarci jana’izar akwai Alhaji Kunle Saani, Shik Muideen Bello, babban limamin masallacin Ibadan, Sheik Abubakri Abdulganiyu Agbotomokere da sauransu.
Ya mutu ya bar mace daya Florence Ajimobi da kuma yara biyar. Daya daga cikin ‘ya’yansa Idris Ajimobi ya auri ‘yar gidan gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, wato Fatima.

Leave a Reply

Your email address will not be published.