Mahaifi ya yi wa yar sa fyade har tayi ciki

Wani mutum mai shekaru 61 da yayi shekaru yana zina da ‘yar cikinsa har ta dauki ciki ya shiga hannu.

Tun sadda yarinyar ke ‘yar karamar uban nata ya fara lalata da ita, sannan ya ci gaba har ta kai shekaru 19 inda ta dauki juna biyu.
Yarinyar ta ce mahaifin nata da yayi ta kwanciya da ita ba da son ranta ba, ya yi barazanar yi mata dukan kawo wuka idan ta sake wani ya sani.
Ta ce bayan mahaifin nata ya gano ta dauki ciki sai yakai ta wani kantin sayar da magani akayi mata allurai aka kuma ba ta magani domin ta sha cikin ya zube.
Dubun mahaifin ta cika ne bayan yarinyar  ta kai kokenta wajen kungiyar kare hakkin mata da yara ta FIDA, wadda ta sanar da ‘yan sanda.
Kakakin ‘yan sandan jihar Legas, Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa rundunar na bincikar tsohon, yayin da aka kai yarinyar cibiyar kula da lafiya ta Mirabel domin a duba ta.
Ya kara da cewa wani mutum dan shekara 33 yana hannun rundunar bisa zargin sane da yin lalata da ‘yarsa mai shekaru 14.
“Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, yanzu haka muna shirin gurfanar dashi a gaban kotu.
“Mun kai yarinyar mai shekaru 14 cibiyar kula da lafiya ta Mirabel domin ba ta kulawa”, inji shi.
Bala Elkana ya ce sun kame wadanda ake zargin ne duk a cikin watan Yuni. Wanda yayi wa diyarsa ciki a unguwar Ikorodu, shi kuma na biyun a yankin Barga

Leave a Reply

Your email address will not be published.