An gurfanar da Telan da yayi wa ƴan mata biyu fyaɗe a gaban kotu

Rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti ta gurfanar da wani Tela mai shekaru 27 mai suna Taiwo Odetunde a gaban wata kotun majistare da ke Ado-Ekiti.

An zargi telan da jan yara mata biyu masu shekaru 13 da 14 inda ya yaudaresu da alkawarin cewa zai dinka musu takunkumin fuska sannan yayi musu fyaɗe.
‘Yar sanda mai gabatar da kara, Monica Ikebuilo, ta sanar da kotun cewa wanda ake karar na fuskantar zargi a kan fyade kuma ya aikata laifin ne a ranar 9 ga watan Yunin 2020 a Ado-Ekiti

Leave a Reply

Your email address will not be published.