Iran ta ba da sanarwar kama Donald Trump

Iran ta ba da sanarwar kama Donald Trump

Iran ta bayar da sanarwar kama shugaban Amurka Donald Trump kan kisan babban kwamandanta Janaral Qassem Soleimani.
Hukumomin Iran sun ce Mista Trump da wasu mutane sama da 30 za su fuskanci tuhumar kisan kai da kuma ta’addanci, sun kuma nemi agajin ‘yan sandan kasa da kasa a shari’ar da za’ayi.
An kashe Janaral Soleimani a wani harin sama da dakarun Amurka suka kai Baghdad babban birnin kasar a watan Janairu.
Masu sharhi sun ce umarnin kamun kawai wata magana ce ta fatar baki wadda ba za ta yi tasiri ba, sai dai yana nuna wata tsantsar kiyayyar da shugabancin Iran ke yi wa Donald Trump
Babban mai shigar da kara na Iran Ali Alqasimehr ya ce: ”An gano kusan mutum 36 da ke da hannu a kisan Hajj Qasem. Sun sa ido kan aikata kisan, sun kuma ba da umarni,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Mehr ya ruwaito shi yana cewa.
”Wannan ya hada da jami’an siyasa a na soja daga Amurka da ma wasu kasashen, wadanda bangaren shari’a ya aike musu sammaci kuma aka kuma sanar da hukumar ‘yan sanda ta kasa da kasa.”
Mista Trump yana gaba-gaba a jerin kuma za a ci gaba da kokarin kama shi ko da bayan ya sauka da shugaban kasa, a cewar mai shigar da karar.
Mataimakin Ministan Harkokin Waje Mohsen Baharvand ya ce nan ba da dadewa ba bangaren shari’ar Iran zai aika sammaci ga mutanen da ke da hannu a kisan Janar Soleimani, kuma yana fatan ya gano wadanda suka yi amfani da jirgi marsa matukin, in ji kamfanin dillancin labaran Isna.
“Iran ba za ta daina wannan kokari ba har sai an gurfanar da mutanen a gaban shari’a,” kamar yadda ya ayyana.
Sanar da hukumar ‘yan sanda ta kasa da kasa na nufin aike bukata ga hukumomin tsaro a aksashen duniya don nemo tare da kama wanda ake nema. Amma ba sammacin kamu ba ne na kasa da kasa.
Wakilin Amurka na musamman Brian Hook ya ce: ”A nazarinmu, hukumar ‘yan sanda ta kasa da kasa ba za ta shiga lamarin ba kuma an sanar da su ba bisa tsarin dimukuradiyya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.