Najeriya ta ɗauki Matakai 8 domin daƙile yaduwar korona

 

Najeriya ta ɗauki Matakai 8  domin daƙile yaduwar cutar korona

Gwamnatin Najeriya ta sake gabatar wa ‘yan kasar sabbin matakai kan kullen annobar cutar korona.
Hakan na zuwa ne bayan wata guda da bayyana matakin sassauta dokar kulle karo na biyu da kwamitin yaki da annobar korona da shugaban kasar Najeriya ya yi a ranar 28 ga watan Mayu da ya gabata.
A ranar Litinin ne kwamitin ya kara yin bayani ga ‘yan kasar kan ci gaban da aka samu da kuma sabbin matakan sassaucin da za a dauka a nan gaba.
Mafi yawan sabbin matakan za su fara aiki ne daga daya ga watan Yuli mai kamawa kamar yadda Shugaban kwamitin kuma Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana.
Kwamitin ya ce an samu karuwar kamuwa da cutar cikin gaggawa a Najeriya daga adadin masu cutar 8,915 a ranar 28 ga watan Mayu zuwa 24,567 a ranar Litinin 27 ga watan Yuni.
Daga cikin sabbin matakan da kwamitin shugaban ƙasa da ke yaƙi da annobar korona a Najeriya ya sanar sun haɗa da ɗage haramcin tafiye-tafiye tsakanin jihohi amma a lokutan da dokar takaita zirga-zirga ba ta aiki.
A cewar kwamitin dole ne duka tasoshin mota zu zama suna da na’urar auna zafin jiki da kuma tabbatar da ko wanne fasinja sai ya sanya takunkumi kafin ya shiga mota. Za kuma a fitar da wasu dokokin da ake bukatar duka tashoshin kasar su kasance suna bi.
A baya dai kwamitin ya ce an sanya dokar takaita zirga-zirga a fadin kasar daga karfe 10 na dare zuwa 4 na safiya kuma dokar za ta ci gaba da kasancewa a haka.
Kwamitin ya ce za dokar kasuwanni za ta kasance kamar yadda ta ke a yanzu a fadin kasar.
Kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar korona a Najeriya ya sanar da matakin rufe kananan hukumomi 18 cikin 774 da ke Najeriya.
A cewar kwamitin, wadannan kananan hukumomin su ne suke da kashi 60 cikin 100 na mutum 24,077 da suka harbu da cutar korona
Sauran matakan sun da haɗa da:
1: Za a bude zirga-zirgar jiragen sama na cikin gida nan gaba amma kwamitin bai bayyana lokacin hakan ba
1: Za’a Bude makarantu ga daliban da za su rubuta jarrabawar karshe wadanda suka hadar da ‘yan SS3 da JS3 da kuma Firamari 6
3: Gidajen cin abinci za su ci gaba da kasancewa a kulle sai dai wadanda suke yi wa otel-otel girki
4: Dakunan haska fina-finai da wuraren motsa jiki suma za su ci gaba da kasancewa a rufe
5: Mutane 20 ne kawai aka yarda su halarci jana’iza ko kuma daurin aure
6: Ma’aikatan gwamnati za su ci gaba da aiki daga karfe 9 zuwa 2 na rana kamar yadda suke yi a yanzu
7: Tilasta amfani da takunkumi a taron jama’a
8: Samar da abin wanke hannu da sabulu a wuraren taron jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published.