Najeriya za ta bude makarantu ga ɗaliban da za su rubuta jarabawa

Shugaban kwamitin kuma Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya kuma ce za a bude makarantu ga daliban da ke shirin rubuta jarrabawa – ‘yan aji shida a firamare da ‘yan aji uku na karamar sakandare da kuma ‘yan aji uku na babbar sakandare.

Hakazalika, gwamnatin tarayyar ta amince da bude shige da fice tsakanin jihohin kasar nan, amma matukar ba a zarta lokutan doka ba.
Gwamnatin tarayyar ta ƙara da amincewa da sauka ta tashin jiragen sama a cikin fadin kasar nan kadai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.