Yarabawa sun fara zuga Tinubu

Sakamakon zaton da mutane da yawa su ke yi a kan cewa abubuwan da su ka afku a Jam’iyyar APC a cikin ‘yan kwanakin nan suna nuni ne da cewa akwai wata ‘yar tsama a tsakanin Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da kuma jagoran jam’iyyar na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, da alama kungiyar Yarabawa ta Afenifere na neman tunzura jagoran jam’iyyar na kasa kuma dan kabilarta, wato Tinubun.

daya daga cikin shugabannin kungiyar al’adun ta Yarabawa, Cif Ayo Adebanjo, ne ya yi zargin cewa, shi tun asali ya na da masaniyar Shugaba Buhari da ma ya na yaudarar Tinubu din ne kan zaben 2023 da ke tafe.
Adebanjo ya ce, jagoran jam’iyyar shi ma yaudarar shugaban kasar ne ya ke yi a inda ya kwatanta gayyar jam’iyyar ta APC da cewa gayya ce ta mutanen da sam ba su dace da junansu ba.
Duk da cewa fadar Shugaban kasar ta fito tana shelanta wa duniya cewa babu wata baraka a tsakanin shugaba Buhari da Tinubu din, amma da yawan masu sharhin al’amurran yau da kullum sun kwatanta shawarar da kwamitin shugabannin jam’iyyar ya zartar a ranar Alhamis ta rushe kwamitin gudanarwan jam’iyyar a matsayin kai wani mummunan hari ne ga Tinubu din, wanda ake da tabbacin yana goyon bayan tsohon shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole da aka sauke.
Akwai dai rade-radin da su ka yawaita masu nuni da cewa Tinubu, wanda tsohon gwamnan Jihar Legos ne yana hararan kujerar shugabancin kasar nan a shekarar zabe ta 2023, wanda kuma abubuwan da suka faru din a cikin jam’iyyar na kwanan nan duk abubuwa ne da suke nuni da kafa shinge ga bukatar na shi.
1: Adebanjo ya ce, “Ina cikin damuwa da lamurransa (Tinubu). Duk ya san da wadannan abubuwan, amma kuma duk da hakan ya tsaya yana mai dogaro da Buhari din yana yi masa aiki domin ya maishe shi shugaban kasa. Tun can baya na fito na fada cewa Buhari yana yaudarar Asiwaju Tinubu ne kawai, shi ma kuma Asiwaju yana yaudarar Buhari din ne kawai. Kowa so ya ke kawai ya yi amfani da dan’uwansa wajen cimma manufarsa. Me ya sanya Tinubu ya soki batun sake fasalin kasa bayan kuma ya san wannan shi ne abin da ya kai Buhari kujerar mulki?
Ina cikin harkokin siyasa tun a shekarun saba’inoni. Lokacin da da yawan masu surutu a halin yanzun ba a ma haife su ba. Wannan shi ne gaskiyar lamarin, hatta Buhari a wancan lokacin yana dan karamin yaro ne. A yanzun yana shekarun haihuwa 74. Duk lokacin da na shaida maku cewa, me ya sanya Tinubu, Mataimakin shugaban kasa (Yemi Osinbajo), da duk wadanda su ke cikin hadakar rajin kare Dimokuradiyya su ke fadawa cikin jam’iyyar APC? Me ya sanya a halin yanzun su ke gogoriyon tsayuwa a kan batun sake fasalin zamantakewa a kasar nan? ba su iya cewa komai.
Duk abin da nake fada maku a halin yanzun ba wani abu ne sabo ba, abu ne da na saba fadansa. Na ce da Jagaban (Tinubu) da Osinbajo, ya kamata su fice daga cikin jam’iyyar APC. Na fadi hakan a sarari. Wannan abin da ya faru din abin kunya ne ga al’ummar Yarabawa. Abin da ya faru din a halin yanzun ya nuna cewa sam babu wani abin da ya maishe su tsintsiya madaurinki daya.”
2: Cikin wata sanarwa da ya fitar mai shafuka Bakwai, Tinubu ya kore jita-jitar cewa rusa kwamitin gudanarwa da kwamitin shugabannin jam’iyyar APC ya yi a wajen taronsa wanda shugaban kasa ya jagoranta kuma manyan jami’an gwamnati ma duk suka halarta da sauran shugabannin jam’iyyar an yi shi ne da nufin kalubalantar aniyarsa ta neman shugabancin kasar nan kamar yadda ake rade-radin hakan a shekarar 2023.
Tinubu wanda ba shi cikin kwamitin shugabannin, ya karfafa cewa har yanzun bai yanke shawara ba tukunna game da makomar na shi a shekarar zabe ta 2023, lura da matsalar tattalin arziki wanda annobar korona ta haifar, wacce kuma ta harbi akalla mutane 24,077, sannan kuma ta kashe mutane 558 a cikin kasar nan ya zuwa ranar Asabar da ta gabata.
Ya ce a maimakon ya tsayu a bisa harkokin siyasar ta shekarar 2023, ya gwammace ya sadaukar da lokacinsa ne a cikin ‘yan watannin da suka gabata yana nazarin tsare-tsaren da za su iya taimaka wa kasar nan wajen fitar da ita daga yanayin da take a cikinsa a halin yanzun.
Tinubu wanda ya yi rashin daya daga cikin makusantarsa kuma tsohon gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, wanda ya rasu a sakamakon kamuwa da annobar ta korona a ranar Alhamis, ya bayyana cewa yana ganin sam bai dace ba a halin yanzun ya tsaya yana Magana a kan abin da ka iya faruwa a nan da shekaru uku masu zuwa bayan kuwa akwai abubuwan da suka addabi kasa a halin yanzun. 2023 ita za ta bayar da amsar kanta da kanta a lokaci na gaba,” in ji Tinubu.
3: Tinubu ya kara da cewa, ya yi wa jam’iyyar APC aiki matukar iyawansa fiye da kowa ko fiye da yawancin mutane.
Don haka sai ya yi roko ga wakilan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar da aka sauke da kuma dukkanin ‘ya’yan Jam’iyyar da kowa ya hakura a zauna lafiya.
Tinubu ya kuma yaba wa tsohon shugaban jam’iyyar na kasa da aka sauke, da dukkanin wakilan rusasshiyar kwamitin gudanarwan jam’iyyar a bisa irin gagarumin nasarorin da jam’iyyar ta samu a karkashin jagorancinsu, musamman yadda suka tabbatar da nasarar sake zaben shugaban kasa Buhari, sai ya nemi Oshiomhole da ya karbi kurakuransa.
Tinubu ya ce yana da tabbacin Oshiomhole ya yi bakin kokarinsa, sai dai duk kokarin na shi ya zo ne a makare.
4: Tinubu ya kara da cewa, yana sa ran duk wasu sabani a cikin jam’iyyar za a warware su a cikin ruwan sanyi, wadanda har suka kai ga zuwa kotuna wanda bai kamata ba, abin da shugaban kasa, shi kansa da tsohon shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar Cif Bisi Akande, duk suka yi suka a kansa.
Ya kuma yi kira ga Oshiomhole da ya mara wa dan takaran jam’iyyar a zaben gwamnan Jihar Edo da ke tafe, Pasto Osagie Ize-Iyamu, baya.
Fadar shugaban kasa ta nanata fadin cewa, ko kusa babu wata takun saka a tsakanin shugaban kasa da Asiwaju Tinubu.
Babban mai taimaka wa shugaban kasa a kan harkokin manema labarai da wayar da kai, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Asabar, ya ce bukatar da Buhari ya gabatar wa kwamitin shugabanni na jam’iyyar APC wacce kuma bakidaya kowa ya yi na’am da ita, ya yi ta ne domin ceto jam’iyyar wacce a wancan lokacin take fuskantar wani rikici mai ban tsoro.
5: A  kan bayar da wannan shawarar, ya ce Shugaba Buhari ya yi abin da tsarin mulkin jam’iyyar ya nemi da kowa ya yi ne na yin tafiya a tare da kowa.
Ya ce abin da Buhari din ya yi ya zama karbabbe sosai ga dukkanin ma’abota tafiyar Dimokuradiyya da kuma ‘ya’yan jam’iyyar, fadar shugaban kasa ta shiga damuwa ne a bisa yadda wasu su ke kokarin nuna cewa wai Buhari yana kalubalantar Tinubu ne.”
Shehu ya ce tun asali a wajen kafa jam’iyyar APC da Buhari da Tinubu duk sun zaku ne wajen ganin Dimokuradiyya ta yi aiki a bisa kishin kasa.
Sanarwar ta kara da cewa, “Akwai tuntubar juna a tsakaninsu (Buhari da Tinubu), dangantakar su kuma tana nan da karfinta, su kadai suka san yadda su ke tafiyar da al’amarinsu a tsakaninsu.”
A wani rahoton kuma, tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Mista Adams Oshiohmole, da sauran wakilan rusasshen kwamitin gudanarwar jam’iyyar su 16 sun bayar da kai bori ya hau a halin yanzun sun janye karar da suka shigar a gaban kotu, sun kuma amshi rushe su da aka yi.
6: A wajen wani taron manema labarai a Abuja ranar Asabar, Oshiomhole ya shelanta cewa, biyayyarsa ga Shugaban kasa Buhari da kuma jam’iyyar ta APC wacce a halin yanzun take a karkashin jagorancin kwamitin Gwamna Mai Mala Buni.
Ya ce, a karshen taron kwamitin shugabannin jam’iyya da duk ku ka sani, an rushe kwamitin gudanarwa wanda hakan ke nuni da cewa a yanzun kuma ba ni ne shugaban jam’iyyar APC na kasa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.