Ganduje ya janye dokar kulle tare da buɗe duk gurin da aka kulle a Kano

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya bada izinin janye dokar hana zirga zirga ta ranaku wanda aka saka saboda annobar Corona wato Covid-19, amma har yanzu akwai dokar hana fita daga karfe 10 na dare zuwa karfe 4 na asubah. 

Wannan yana nufin mutane zasu iya fita harkokin su daga karfe 4 na asubah har zuwa karfe 10 ma dare.
Gwamnatin ta ce ma’aikata daga mataki na 12 zuwa sama za su koma aiki daga ranar Litinin 6 ga watan Yuli.
Sannan ana ci gaba da tattaunawa kan ranar da za a bude makarantu ga dalibai da ke shekarar karshe da masu rubuta jarrabawar kammala aji uku da ‘yan firamare masu rubuta jarabawar shiga sakandare.
Haka zalika cire wannan doka na nuni da cewar an bude dukkan guraren da aka kulle a baya amma dole su tabbatar da matakan kariya a guraren harkokinsu kamar yadda hukumomin lafiya suka umarta, a cewar kwamishinan yada labarai na Kano Malam Muhammad Garba
    

Leave a Reply

Your email address will not be published.