Ganduje ya umarci ƴan kwangilar da ke aiki a gwamnatinsa su koma wuraren ayyukan su nan take

Gwamnan jihar kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya umarci dukkan ƴan kwangilar da ke aiki a gwamnatin jihar kano su koma wuraren ayyukan su nan take.

 Ya ce hakan ya zama dole ta hanyar fahimtar cewa rayuwa dole ne ta cigaba bayan bullar cutar coronavirus, saboda haka ya shawarci mazaunan jihar da su koyi zama tare da kwayar cutar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin fara taron majalisar zartarwa na jihar, wanda ya mai da hankali kan sake duba kasafin kudin wannan shekarar da sauran batu tuwa.
Gwamnan ya kuma ba da umarnin bude dukkanin kamfanoni masana’antu a cikin jihar, “don ci gaba da kula da bangaren ci gaba a cikin jihar.
“Tare da hakan, duk ma’aikatan kamfanoni, na iya ci gaba da samun abin da suke karba (Albashi)”
Kasafin Kudin, wanda Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi, Nura Muhammad Dan kadai ya gabatar, an ba da fifiko a fagen ilimi, kiwon lafiya da kayayyakin more rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.