Majalisar zartarwa ta sahhalewa Ministoci 4 Naira Biliyan 20 domin yin wasu ayyuka

Majalisar zartarwa ta sahhalewa Ministoci 4 Naira Biliyan 20 domin yin wasu ayyuka

A taron FEC da ake yi kowane mako, gwamnatin tarayya ta amince da ware kudi N20, 366, 454, 990 domin yin wasu ayyuka na gyara hanyoyi da wani titin jirgin sama a zaman jiya.
Gwamnatin tarayya za ta kashe wannan kudi ne a ma’aikatu hudu kamar yadda mu ka samu labari daga gidajen jaridun Najeriya a ranar Laraba, 1 ga watan Yulin 2020.
Bayan kammala ganawar shugaban kasa Muhammadu Buhari da jami’an gwamnatinsa, da wasu Ministoci sun bayyyana cewa takardun da suka gabatar a majalisar FEC sun samu shiga.
Ministan ayyuka da gidaje, Baba Tunde Fashola; Ministan babban birnin tarayya, Mohammed Bello; Ministan harkar ruwa, Suleiman Adamu da ministan harkokin jiragen sama, Hadi Sirika, su ka bayyana wannan.
Mohammed Bello ya ce an yi na’am da wasu takardu biyu da ya gabatar gaban shugaban kasa na yin titi daga Yaba zuwa Gurdi a cikin yankin Abaji da kuma aikin hanyoyi a cikin garin Abaji.
    “Kwangila ta biyun aikin tituna ne a garin Abaji da ke kudancin birnin tarayya Abuja. Titunan sun kai tsawon kusan kilomita 8.4, za suci N2, 128, 176,102.50, ana sa rai a gama cikin watanni shida.” inji Bello.
Sanata Hadi Sirika ya ce gwamnatin tarayya ta amince da aikin hanyar motocin haya a cikin babban filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas. Aikin zai ci Naira biliyan 2.3
Ma’aikatar ruwa ta gabatar da takardun neman kwangilar gyara cibiyar noman rani da ke garin Lankang, jihar Filato. FEC ta amince da wannan kwangila a kan Naira miliyan 634.2.
Baba Tunde Fasola ya gabatar da takardu biyu ne wadanda duka aka amince dasu. “Takardar farko aikin titi ne na iyakar Koton-Karfe-Lokoja na hanyar Abuja-Abaji-Lokoja a kan Billiyan 3.076.”
“Na biyu kuma titin Cham-Numan ne a kan babban hanyar Gombe-Yola. Wannan aiki zai ci Biliyan 7.607.” Gaba daya wadannan ayyuka da za ayi, za su tashi a kusan Naira biliyan 20.4

Leave a Reply

Your email address will not be published.