Bashin da ake bin Najeriya ya tashi daga Naira Tiriliyan 27.4 zuwa Naira Tiriliyan 28.63

Bashin da ake bin Najeriya ya haura N28.63 Trillion – cewar  Ofishin kula da basussukan Najeriya 

Jimillar bashin kudin da ake bin Najeriya ya haura Naira Tiriliyan 28,63 (N28.63tn), ofishin kula da basussukan Najeriya DMO ce ta sanar ranar Alhamis. 
A rahoton basussukan kasar da aka saki a daren alhamis, ofishin DMO ta yi bayanin cewa jimillar bashin da ake bin Najeriya ya tashi daga N27.4tn a Disamban 20019 zuwa N28.63tn a Maris 2020.
 Hakan ya nuna cewa cikin watanni uku , bashin da Najeriya ta ci ya karu da N1.23tn. 
Yayinda N9.99tn daga ciki bashin da aka karbo daga kasashen waje ne, Sannan N18.64tn da aka karba daga hannun bankunan cikin gida. 
 Rahoton da ofishin DMO ya fitar ya kara nuna cewa: Najeriya ta kashe N609.13 billion wajen biyan wani sashen basussukan tsakanin watan Junairu zuwa Maris, 2020.
 Lissafin wata-wata ya nuna cewa an biya N251.35 billion a Junairu, Sannan N158.12 billion a Febrairu, kuma N199.658 billion a watan Maris. 
A cikin wadannan watanni uku, kudin shigan da gwamnatin tarayya ta samu sune N950.56 billion amma ciki an yi amfani N943.12 billion wajen biyan bashi.
 Idan za ku iya  tuna cewa Bankin bada lamuni na duniya IMF ya ce Najeriya za tayi amfani da dukkan kuɗadɗen shigan da zata samu a shekarar 2020 wajen biyan kuɗin ruwan bashi. 

Leave a Reply

Your email address will not be published.