Ƴar shekara 14 ta gudu daga gidan iyayenta zuwa wurin saurayin facebook da zama

Yarinya mai shekaru 14 ta gudu daga gidan iyayenta zuwa wurin saurayin ta na ‘facebook’

  Wata yarinya ‘yar shekaru 14 ta gudu daga gidan iyayenta da ke Biogbolo a karamar hukumar Yenagoa ta jihar Bayelsa domin kasancewa tare da saurayinta, Victory Age, mai shekaru 17 wanda suka hadu a dandalin sada zumunta na ‘Facebook’.
 Sai dai, rundunar ‘yan sanda ta yi nasarar kama Age tare da abokansa, tare da yin holinsu a hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa da ke Yenogoa a ranar Alhamis.
 Rundunar ‘yan sanda tana zargin matashin mai shekaru 17 da laifin boye yarinyar mai shekaru 14 na tsawon wata guda ba tare da izinin iyayenta ba. 
Wasu rahotanni sun bayyana cewa karamar yarinyar ta zabi guduwa zuwa wurin saurayin ne saboda mugun zaman da ke tsakaninta da matar mahaifinta. 
Yarinyar, ‘yar aji 4 a makarantar sakandire, ta ce ba ta sanar da kowa ba kafin ta bar gida, kawai ta bar rubutaccen sakone a dakinta kafin ta tafi. 
Ta amince cewa Age da abokinsa suna kwanciya tare da ita a tsawon zamansu na wata guda, ta bayyana cewa ba tilasta mata suke yi ba, da amincewarta ake yin komai. 
” Ta ce Na ziyarci abokina a Onopa bayan haduwarmu a ‘Facebook’. 
“Shi kansa ya girgiza da ya ganni da jakar kayana.
 Ya tambayeni me yasa na dauko jakar kaya, sannan me nake nufi?, nan take na bashi amsar cewa zan zauna tare dashi na tsawon sati guda. 
“Ya tambayeni ko iyayena ba za su nemeni ba, sai na ce ‘Eh’. 
Daga nan sai muka tafi wani Otal inda mu ka zauna na tsawon kwanaki uku kafin daga nan mu koma wurin abokinsa. 

Leave a Reply

Your email address will not be published.