Majalisar Ɗinkin duniya ta dakatar da kai tallafi Arewa maso gabas

Majalisar Ɗinkin duniya ta dakatar da kai tallafi Arewa maso gabas, Bayan da Boko Haram sukayi kokarin ɓaro jirginta, 

Majalisar ɗinkin duniya ta dakatar da kai agaji da tallafi a jirgin sama sakamakon yunkurin da akayi na ɓaro jirginta mai saukar Angulu a jihar Borno.
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutuwar mutane biyu, ciki harda Mai shekara biyar, ya yinda Wasu da-dama Suka jikkata.
Najeriya ta Sami sabon jirgin yaƙi me leƙen Asiri
Wannan ya biyo bayan ruwan harsasan da maya ƙan Boko Haram masu yunkurin shiga garin Damasak suka kai wa jirgin majalisar dinkin duniya a ranar Alhamis.
Shugaban shirin tallafi da bada agaji na majalisar dinkin duniya dake nan Najeriya, Edward Kallon, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Asabar, a shafinsa na twitter.
Edward yace: “Duk da cewa har yanzu muna duba abinda ya faru, mun tabbatar da cewa akwai alaman harbin harsasai jikin ɗaya daga cikin jirage mai saukar angulu yayinda ya nufi Damasak.”
“Jirgin ya samu nasarar juyawa kuma ya koma Maiduguri. An ci sa’a babu wanda ya ji rauni cikin matuƙan jirgin, kuma babu fasinjoji ciki a lokacin.”
“Amma, dubi ga irin haɗarin da abinda ya faru, kuma bisa shawarar UNDSS da UNHAS/WFP, na dakatar da shirin agaji da jinkan UNHAS a Arewa maso gabas, domin bamu daman tattaunawa da gwamnati wajen duba tsaron jiragenmu da kuma ganin yadda za’a kiyaye gaba.”
SOJIN SAMA sun ragar-gaza ƴan boko haram
Edward Kallon ya ce wannan dakatarwar na tsawon makon daya ne. Bayan mako daya za’a sake duba lamarin.
Ya ce cikin mako dayan, agajin gaggawa da kwashe wadanda rayukansu ke cikin haɗari zai kasance ɗaya-ɗaya ne kuma da umurnin shugaba.
Shirin lamunin abincin duniya WFP ke gudanar da sufurin jirgin saman domin taimakawa wajen safarar ma’aikatan kungiyoyin tallafi da jinkai zuwa wurare masu hadari kuma kan farashi mai sauki.
Haka zalika jiragen na taimakwa kai agajin gaggawa ga wadanda hari ya rutsa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published.