Sojin sama sun ragargaza sabbin shugabannin Boko Haram

Sojin sama sun ragargaza sabbin shugabannin Boko Haram

 Dakarun sojin saman Najeriya sun halaka mayakan Boko Haram masu tarin yawa da kayan aikinsu a harin da rundunar Operation Lafiya Dole ta kai Mina, kusa da Gulumba da kuma yankin Gana-Kumshe a yankin arewacin jihar Borno.
 Wannan ragargazar da dakarun suka yi wa mayakan ta’addancin ta hargitsa su tare da halaka sabbin shugabanninsu.
 Hakan ya faru ne a ranar 3 ga watan Yulin 2020. Bayan rahotannin sirrin da rundunar sojin ta samu na wurin da mayakan suka koma da kuma inda kayan aikinsu suke.
 Ta jiragen yaki dakarun suka tabbatar da ingancin zancen. 
Babu jimawa sojojin suka dinga jefawa wuraren bama-bamai, lamarin da ya kawo halakar mayakan ta’addancin masu tarin yawa tare da wata bukkar kayan aikinsu wacce ta kama da wuta. 
Wasu daga cikin mayakan da suka samu tserewa an bi su tare da halaka su.
Najeriya ta Sami jirgin yaƙi na leƙen Asiri
 Shugaban sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar , ya jinjinawa sadaukarwar ATF da kuma kwarewarsu. 
Hedkwatar tsaro ta kasa, ta kara da kira garesu da su tsananta takura ‘yan ta’addan tare da duk wani nau’in ta’addanci da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron kasar nan. 

Leave a Reply

Your email address will not be published.